Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana Nijeriya da wasu kasashe 11 a matsayin wadanda ke fuskantar hadarin yunwa mai tsanani, matukar ba a dauki matakan gaggawa ba.
A wani rahoto da Hukumar Abinci da Aikin Noma (FAO) da WFP suka fitar ranar Litinin, an bayyana cewa rikice-rikice, matsalolin tattalin arziki da sauyin yanayi suna kara jefa miliyoyin mutane cikin yunwa a duniya.
Kasashen da ke cikin hadarin mafi tsanani sun hada da Gaza, Sudan, Sudan ta Kudu, Haiti da Mali.
Rahoton ya gargadi cewa cikin watanni biyar masu zuwa, halin zai kara tabarbarewa idan ba a samar da agaji da kudaden jin kai cikin gaggawa ba.