Nijeriya ta zama ƙasa ta uku wajen karbar bashin Bankin Duniya bayan karuwar karbar rancen sama da dala biliyan biyu daga 2023 zuwa 2024.
A cewar Bankin Duniya bashin da Nijeriya ke karba ya karu zuwa kaso 14.
Abin da ke haska adadin bashin da kasar nan ta ciyo ya tashi daga dala biliyan 14.3 a 2023 zuwa dala biliyan 16.5 a 2024.
Karuwar wannan kaso ne ya sanya Nijeriya ta zama kasa ta uku a duniya da ta tafi karbar bashin Bankin Duniya.
A cewar bankin, kasar Bangladesh na ci gaba da rike matsayinta na farko a matsayin mafi cin bashin bankin duniya, sai kasar Pakistan da take matsayinta na biyu da adadin bashin.
Bayanai daga ofishin lura da basuka kasa, ya nuna cewar bashin da Bankin Duniya ke bin Nijeriya ya kai dala biliyan 15.59 a watan Maris na 2024.
Wannan na zuwa daidai lokacin da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ke kara dogaro da tallafin kudi daga kasashen waje yayin da ake fuskantar matsin tattalin arziki a kasar.