NiMET, ta fitar da sabon hasashen yanayi inda tace da yiwuwar ɓarkewar cututtukan ruwa a karshe shekara 2025
Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa, NiMET, ta fitar da sabon hasashen yanayi na shekarar 2025, inda ta yi kashedi game da yiwuwar ɓarkewar cututtukan ruwa kamar kwalara da gudawa a jihohi da dama sakamakon ruwan sama mai yawa da ambaliya da ake sa ran zai faru. ya bayyana jihohin Lagos, Abuja, Kaduna, Ebonyi, Cross River, Abia da Akwa Ibom a matsayin wuraren da ke da haɗari mafi tsanani, musamman a yankunan da ke fama da matsalolin tsaftar muhalli da yin bayan gida a fili.
Hukumar ta kuma nuna damuwa kan yawaitar zazzabin cizon sauro, cutar numfashi, da matsalolin da suka shafi zafi kamar bugun zuciya da kumburi sakamakon canjin yanayi, tana mai cewa yankunan kudanci kamar Lagos da Bayelsa na iya fuskantar kwanaki har 290 na ruwan sama. A yayin da galibin ƙasar zai fuskanci ruwan sama matsakaici zuwa ƙasa da matsakaici, wasu sassan kamar Kaduna da Abuja za su fuskanci sama da matsakaicin ruwa, yayin da kuma ɓangaren arewa zai fuskanci ruwan sama tsakanin milimita 405 zuwa milimita 1,500, wanda zai ƙare daga watan Oktoba zuwa Disamba.