Kungiyar ‘yan kwadago ta Najeriya NLC ta yi watsi da shirin gwamnatin kasar na yunkurin kara farashin man fetur, in da ta ce ba za ta fada gadar zaren da gwamnatin ƙasar ke neman shiryawa mutanenta ba.

Cikin wata sanarwa da NLC ta fitar shugaban kungiyar Kwamared Ayuba Wabba ya ce sanarwar da shugaban NNPC Malam Mele Kyari ya yi ta kara farashin man fetur zuwa 340 daga watan Fabirairu ba ta yi wa ‘yan kasar dadi ba.

Cikin sanarwar NLC ta ce cewa za a rabawa ‘yan Najeriya miliyan 40 naira 5000 domin rage musu radadin karin farashin man fetur ‘abin dariya ne’, inda ta ce idan aka lissafa kudin sai ya haura na tallafin man fetur din da ake bayarwa a kasar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: