Nuhu Toro ya roƙi gwamnati da ta biya duk hakkokin da kungiyoyin kwadago suke bi tun watan Fabrairu

0 148

Sakataren kungiyar kwadago ta kasa, Nuhu Toro, ya roƙi gwamnatin tarayya da ta biya duk wasu hakkokin da kungiyoyin kwadago suke bi tun watan Fabrairu.

Kungiyoyin da abin ya shafa sun haɗa da PENGASSAN, da Ƙungiyar Ma’aikatan Gine-gine da reshen PENGASSAN a Kaduna da sauransu.

Toro ya yi wannan roƙon ne yayin zanga-zangar lumana da wasu ‘ya’yan ƙungiyoyin suka gudanar a gaban Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya a Abuja, inda ya bayyana rashin jin daɗinsa game da yadda darajar Naira ke ƙara faɗuwa.

Sai dai Babban Sakataren Harkokin Musamman, Mista Raymond Omachi, ya ce Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya riga ya amince da buƙatunsu, kuma cikin awanni 48 za a warware lamarin.

Leave a Reply