Ofishin cigaban kasashe rainon Ingila zai mika wasu kayayyakin kiwon lafiya ga hukumar lafiya matakin farko ta jihar Jigawa domin inganta harkokin kiwon lafiya a jihar

0 87

Ofishin cigaban kasashe rainon Ingila zai mika wasu kayayyakin kiwon lafiya ga hukumar lafiya matakin farko ta jihar Jigawa domin inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.

Babban jami’in ofishin mai barin gado, Fedilix Ekon ya bayyana haka lokacin da ya kai ziyara ofishin mataimakin gwamnan jiha, Mallam Umar Namadi.

Ya ce ya kai ziyarar ne domin sanarwa da mataimakin Gwamnan cewar zai tafi wani aiki daban, inda ya mikawa mataimakin gwamnan jaddawalin rahoton aikin ofishin na zango-zango, tare da tattaunawa akan batutuwan da suka shafi dorewar ayyukan ofishin.

Fedilix Ekon ya kara da cewar ayyukan hadin gwiwa da hukumar bada tallafi ta kasar Burtaniya da Gwamnatin Jihar Jigawa ya haifar da da mai idanu.

A jawabinsa, mataimakin Gwamnan, Malam Umar Namadi, ya godewa babban jami’in mai barin gado bisa yunkurin sa na mika kayayyakin, inda ya ce zai taimaka wajen bunkasa harkokin lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: