Ofishin jakadancin kasar Sifaniya a Najeriya ya ce ya bayar da gudummawar allurai miliyan 4 da dubu 400 na rigakafin korona

0 58

Ofishin jakadancin kasar Sifaniya a Najeriya ya ce ya bayar da gudummawar allurai miliyan 4 da dubu 400 na rigakafin corona samfurin Johnson & Johnson ga gwamnatin tarayya don dakile yaduwar cutar ta corona.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a yau mai dauke da sa hannun ofishin jakadanci ya fitar a Abuja.

Tawagar ta bayyana cewa bikin mika rigakafin ya gudana ne a harabar Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa tare da tallafin Asusun Agajin Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF).

A cewar ofishin jakadancin, tallafin ya sa Sifaniya ta zama kasa ta uku da ta bayar da allurar rigakafin COVID-19 ga Najeriya.

Ta ce wannan gudummawar ita ce mafi girma da kasar Sifaniya ta baiwa kasa guda a Afirka kawo yanzu.

Taimakon ya kuma sanya Sifaniya a matsayin ta bakwai mafi yawan masu ba da gudummawar alluran rigakafi a duniya, tare da allurai miliyan 70 da suka bayar kawo yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: