Ofishin Kula Da Basussuka Na Kasa Ya Karyata Cewa Najeriya Ta Gaza Wajen Rage Basussukan Da Kasar China Ke Binta

0 155

Ofishin kula da basussuka na kasa ya karyata wani rahoton da kafafen yada labarai suka wallafa cewa Najeriya ta kasa wajen rage basussukan da kasar China ke binta.
Sanarwar da ofishin kula da basussukan ya fitar yau a Abuja ta shawarci jama’a da su yi watsi da rahoton inda tace na karya ne.
Wani rahoto da wata kafar yada labarai ta buga kwanannan ya ruwaito ofishin kula da basussukan na cewa Najeriya ta gaza rage bashin da kasar Sin ke binta, wanda a yanzu ya karu zuwa naira biliyan 110 da miliyan 310 a cikin shekaru biyun da suka gabata.
Ofishin kula da basussukan ya jaddada cewa a yi watsi da rahoton.

Leave a Reply