Ofishin Shirin yaki da fatara na kasa ya yi kira ga matasan dake cikin shirin N-power rukunin C kashi na 2, dasu yi watsi da labaran dake yawo ta kafar sadarwa ta zamani cewar an shigar dasu cikin shirin.

Jamiin kula da shirin na jiha Mallam Mustapha Umar ya sanar da hakan a wata sanarwa.

Yace har yanzu ofishinsa bai samu wani labari ba dake nuni da cewar an fitar da jerin sunayen matasan da aka dauka domin shiga shirin N-power rukunin C kashi na 2 ba, daga ma’aikatar jinkai, kula da annoba da walwalar jama’a.

Mustapha Umar yace da zarar sun sami labarin zasu sanar da matasan da abin ya shafa, inda ya gargadi matasan dasu yi watsi da duk wasu labarai da suka shafi kafar sadarwa ta zamani.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: