Peter Obi Ya Sanar Da Magoya Bayansa Cewa Yana Kan Hanyar Kwato Nasarar Da Suka Bashi
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankulansu tare da jajircewa, yana mai cewa yana kan hanyar da ta dace domin kwato nasarar da suka ba shi.
Peter Obi ya bayyana hakan ne a cikin jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren jiya.
Duk da cewa shine ya zo na uku a zaben shugaban kasa, Peter Obi ya dage kan cewa shi ne ya lashe zaben.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce ya kuduri aniyar gina Najeriya da za ta amfani kowane dan Najeriya.
Ya kuma soki masu zagin sa, yana mai cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba duk da kalubalen da suke jawo masa. Ya kara da cewa, watakila za a iya samun bita da kulli daga masu adawa da samuwar sabuwar Najeriya, amma ba ya tsoron karairayi da farfagandar da ake yadawa a kansa.