Peter Obi Zai Amsa Tambayoyi Dangane Da Faifan Sautin Dake Yawo Dauke Da Muryar Sa

0 70

Gwamnatin tarayya tace akwai tambayoyin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar labour Peter Obi zai amsa dangane da faifan sautin dake yawo, inda aka ji muryar sa da pastor Bishop David Oyedepo.
Bayan lokaci anji dan takarar shugaban kasar shiru, sai dai yace faifan muryar na karya ne, sannan ya kalubalanci gwamnatin tarayya da yada karya domin bata masa suna.
Sai dai a wani taron manema labarai da ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Muhamad ya gudanar a Birnin Landan ya bukaci Obi yayi bayani da abin da yake nufi da sautin muryar na karya ne.
Lai Muhammad yace faifan sautin da ya subuce wani yunkurin amfani da matsayi ne wajen kawo rudani da cusa kabilanci da addinanci cikin siyasa.
Yace wannan shine karon farko da aka taba samun wani dan siyasa ya fito yakin neman zabe baro-baro ta fuskar bangaranci da kabilanci.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya bayar da rahotan cewa ministan zai yi wata ganawa da yan jaridun duniya kan batun a birnin Landan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: