Ragowar ɗalibai da malaman jami’ar gwamnatin tarayya ta Gusau sun shaƙi iskar ƴanci

0 93

Ragowar ɗalibai da malaman jami’ar gwamnatin tarayya ta Gusau a jihar Zamfara da aka sace ranar 22 ga watan Satumban 2023, sun shaƙi iskar ƴanci. Ƴan bindiga sun yi dirar mikiya a ɗakunan kwanansu a yankin Sabon Gida a ƙaramar hukumar Bungudu da ke jihar Zamfara inda suka sace fiye da ɗalibai 20, galibinsu mata. Bayan ƙoƙarin da hukumomin jami’ar suka yi da iyalansu, wasu da aka kama an sake su ne bayan watanni amma 23 sun ci gaba da kasancewa a hannun ƴan bindigar. Sai dai majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa jami’an tsaro ne suka kuɓutar da ragowar ɗaliban Ajiya Lahadi. Majiyar ta ƙara da cewa wasu masu yi wa ƙasa hidima da aka sace a jihar Sokoto suma an kuɓutar da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: