Rahotanni sun ce akalla mutane 100 sun mutu sakamakon barkewar Cutar Sankarau a jihar Jigawa

0 99

Rahotanni sun ce akalla mutane100 sun mutu sakamakon barkewar Cutar Sankarau a Jihar Jigawa, kuma galibin wadanda lamarin ya shafa yara ne ’yan kasa da shekara 11.

Bayanai sun ce tun a watan da ya gabata aka samu bullar cutar a Jihar, sannan ta fi kamari ne a tsakanin Kananan Hukomin Jihar da ke iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Bincike ya nuna cutar ta mayar da wasu da suka kamu da ita a Jihar kurame.

Kauyukan da aka ruwaito cutar ta fi kamari a cikinsu, sun hada da Mele da Dungundun da Kanya Arewa da Dantanoma da suke a yankunan Kananan Hukomin Babura, Gumel, Maigatari da kuma Sule-tankarkar.

An gano sama da mutum 360 ne suka kamu da cutar a fadin Jihar, sannan kimanin 100 daga ciki sun rasu a sakamakonta.

Jami’i a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, Malam Samaila Mahmud, ya tabbatar da barkewar cutar a Jihar.

Sai dai, jami’in ya ce baki daya mutum 257 ne suka kamu da cutar, yayin da cutar ta kashe mutum 65.

Leave a Reply

%d bloggers like this: