RAMADAN: Gwamnatin jihar Katsina ta ware ₦10Bn domin tallafawa marasa galihu

0 103

Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta ware naira biliyan 10 domin siyan hatsi don tallafawa marasa galihu a cikin watan Ramadan.

Gwamnan jihar Dikko Umar Radda ne ya bayyana hakan a yayin kaddamar da kwamitocin da za su sa ido kan yadda ake rabon hatsin, kamar yadda babban sakataren yada labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed ya bayyana.

Ya ce an yi kokarin rage farashin masara, gero, da dawa zuwa Naira dubu 20 kan kowacce buhu, wanda ya yi kasa da yadda ake sayar da shi a halin yanzu a doron kasuwa.

Ya ce, duk da haka, za a kebe sayan hatsi a matakai goma ga kowane mutum don tabbatar da adalci.

Gwamna Radda ya ce kusan gidaje dubu 400 ne za su ci gajiyar tallafin abinci yayin da tsofaffi da marasa galihu dubu 33 su ma za su sami kayan abinci na kyauta da tallafin kudi.

Gwamnan ya umurci kwamitocin kananan hukumomi da su mika kudaden da aka samu daga sayar da hatsi ga kwamitin jihar domin sakawa a asusun gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: