Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da akayi a watan Fabrairu, Atiku Abubakar, ya shawarci ma’aikatan Najeriya da su kalli ranar ma’aikata ta bana a matsayin lokacin da za su yi tunani da hangen nesa, tare da kiran kada su yanke kauna wajen biyan bukatar su.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa shawarar ta zama wajibi bisa la’akari da dimbin matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta a cikin shekaru takwas na gwamnatin Muhammadu Buhari.
Atiku a sakon da ya aikewa kungiyar kwadago, ya ce rayuwa da jin dadin ma’aikata da iyalansu sun gurgunce, sakamakon kura-kuran manufofin gwamnatin APC mai mulki, wanda ya haifar da rashin tsaro a dukkan bangarori na ma’aikata da suka shafi Rayuwa, Abinci, Matsuguni, Lafiya, Arziki da Ilimi. Sai dai ya umarci ma’aikata da su kasance masu juriya da fata na gari domin karfafawa matasa masu tasowa gwaiwa da kuma makomar kasar nan.