Sojojin Mali sun samu jiragen yaki masu saukar ungulu guda biyu da na’urorin tauraron dan’adam na zamani guda biyu daga kasar Rasha don taimakawa a yakin da suke yi da ‘yan bindiga.

Gwamnatin mulkin sojan da ta kwace mulki a shekarar 2020, ta kara kulla alaka da kasar Rasha, bayan da ta samu sabani da kasar Faransa, wacce tayi mata mulkin mallaka.

A watan da ya gabata ne Faransa ta fara janye sojojinta daga kasar dake yammacin Afirka bayan shafe kusan shekaru 10 suna yaki da masu ikirarin jihadi.

Ana kyautata zaton Sojojin hayar Rasha daga kungiyar Wagner suna taimakawa sojojin Mali, ko da yake gwamnatin mulkin sojan kasar ta ki tabbatar da hakan.

Ministan harkokin wajen Faransa a wata hira da ya yi da France24 a jiya ya ce sojojin hayar na Rasha sun zama alakakai ga sojojin dake mulkin Mali.

Ministan harkokin wajen ya zargi kungiyar Wagner da aikata laifukan take hakkin dan adam da farautar albarkatun kasar Mali.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: