Gwamnatin Jihar Katsina ta ce rashin cika ƙa’ida ne ya sa aka kori ƴan asalin jihar da suka je neman aikin ɗansanda.
A kwanan nan dai aka samu labarin korar wasu matasa ƴan asalin jihar Katsina su 35 da ke neman aikin ɗansanda bayan kwashe watanni a makarantar horas da ƴansanda da ke Kaduna.
To sai dai cikin wata sanarwa da sashen kula da ɗaukar ma’aikata da yi musu ƙarin girma ta Jihar ta fitar, ta ce rashin cika ƙa’idar aikin ne ya sa aka kori atasana.
”Akwai ƙa’idojin da ba su cika ba da suka haɗa da rashin kai tsayin da ake buƙata, da girman kirji da kuma wasu matsalolin lafiya”, in ji sanarwar.
Sanarwar ta tabbatar da cewa mutum 126 ne aka sallama baki daya daga makarantar, amma waɗanda suka fito daga jihar Katsina ba su kai 35 ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa sallamar ta shafi ɗaukacin jihohin Najeriya ba wai jihar Katsina kawai ba, saɓanin yadda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.