Rashin samun isassun kudade na daya daga cikin abubuwan da suka lalata fannin Ilimi a kasar nan – Danzomo

0 77

Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya Da Fasaha ta Jihar Jigawa Dr Lawan Yunusa Danzomo, ya ce rashin samun Isassun kudade na daya daga cikin abubuwan da suka lalata fannin Ilimi a Kasar nan.

Dr Lawan Yunusa Danzomo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Manpower dake Duste.

A cewarsa, bayan zuwan Gwamna Badaru Abubukar, gwamnati Jiha tayi nasarar gano wasu daga cikin matsalolin Ilimin Jihar nan, wanda suka hada da rashin kudade a fannin da rashin gine-gine masu kyau, da kuma karancin Ajujuwa da Malamai.

Haka kuma ya ce gwamnatin Jiha ta kashe Naira Biliyan 20 wajen inganta Ilimin Makarantun Firamare da Sikandiren Jihar nan cikin shekaru 6 da suka gabata.

Kwamishinan ya kara da cewa sunyi nasarar gina Makarantun Firamare 337, da kuma sabbin Kananan Makarantun Sikandire 130 wanda aka kirkira.

Kazalika, ya ce gwamnatin Jiha ta gina sabbin Ajujuwa dubu 6,679 da samar da Kujeru dubu 185,086 da kuma Kujerun Malaman Makaranta dubu 5,963 da aka samar a jihar nan.

Kwamishinan ya ce an gina gidaje 254 ga Malaman Makaranta da kuma Bandakuna dubu 1,418.

Leave a Reply

%d bloggers like this: