

Rikici ya barke jiya a unguwar Sabon Gari cikin birnin Kano a jihar Kano, bayan wasu matasa sun fara kone-kone.
Unguwar ta Sabon Gari wacce yawanci baki ne ke zama a cikinta, ita ce cibiyar rikicin addini da na kabilanci a jihar.
Majiyoyin tsaro sun gayawa manema labarai cewa rikicin ya fara ne lokacin da jami’an Hisbah suka je domin kama wasu a wajen da ake badala kan titin Ballata.
Shaidu sun ce an samu turmutsitsi a kusa da unguwar ta Sabon Gari bayan bata garin sun cinna wa tayoyi wuta.
Sauran majiyoyin sun ce an kashe wasu mutane tare da raunata wasu da dama a rikicin.
An kasa samun jin ta bakin kakakin rundunar yansandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, dangane da batun.