Rikicin da ke faruwa a jam’iyyar PDP ya ɗauki sabon salo

0 89

Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya ɗauki sabon salo bayan ɓangarori biyu sun dakatar da junansu daga jam’iyyar.

Ɓangaren shugaban jam’iyyar na riƙo, Umar Damagun ya dakatar da sakataren watsa labarai na jam’iyyar Dabo Ologunagba, da mai ba jam’iyyar shawara a kan harkokin shari’a, Kamaldeen Adeyemi Ajibade, SAN daga jam’iyyar.

Ana cikin haka ne ɗayan ɓangaren suka fitar da tasu sanarwar, inda suka ce sun dakatar da Umar Damagun da sakataren jam’iyyar, Samuel Anyanwu daga jam’iyyar.

Chinwe Nnorom, daraktan watsa labarai a hedkwatar jam’iyyar ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a jiya Alhamis, inda ta ce “bayan taron majalisar zartarwa na jam’iyyar na 59, an dakatar da sakataren watsa labarai na jam’iyyar, Dabo Ologunagba da mai ba da shawara kan harkokin shari’a, Kamaldeen Adeyemi Ajibade SAN daga aiki, sannan an umarci mataimakansu su cigaba da ayyukansu.” Wannan dai wani sabon babi ne a rikicin babbar jam’iyyar adawar a kan shugabanci wanda aka daɗe ana yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: