

- Yadda yan IPOB suka kashe ‘yan Arewa 10 ciki har da mace mai juna biyu da ‘ya’yanta 4 da wasu mutane 6 a jihar Anambra - May 24, 2022
- Sama da mutane 30 ne aka ruwaito sun bace a jihar Borno bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari - May 24, 2022
- Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya karbi tikitin takarar Sanatan Gombe ta Arewa domin tsayawa takara a jam’iyyar PDP a 2023 - May 24, 2022
Rikicin shugabancin jam’iyyar APC a jihar Kano na kara daukar sabon salo bayan bangaren da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta ya yi watsi da sanarwar uwar jam’iyya kan sulhunta rikicin ‘ya’yanta na jihar.
Matsayar tsagin Sanata Shekarau da ya zabi Alhaji Haruna Dan-Zago a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar Kano na da alaka da bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje jagorancin kwamitin da zai warware matsalar.
A hira da manema labarai jim kadan bayan fitowar sanarwar jam’iyyar APC ta kasa, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce sun yi watsi da wannan sanarwa kuma ba su amince da ita ba.
Sanata Shekarau ya kara da cewa, sanarwar da jam’iyyar APC ta fitar ba ta yi magana a kan matsayar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu ba, sannan jam’iyya ba ta fadi komai tsakanin abin da bangarorin biyu suka bukata ba.