Ministan birnin tarayya kuma tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa rikicin siyasa tsakaninsa da Gwamna Siminalayi Fubara ya zo ƙarshe, bayan wani taron sulhu da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta jiya da dare a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar da aka gudanar a bayan ƙofa, Wike ya bayyana cewa ɓangarorin biyu sun cimma matsaya ta ƙarshe don kawo ƙarshen sabani tare da hada kai domin ci gaban jihar.
Ya ce rikicin ya jima yana gudana, amma yarjejeniyar da aka cimma a daren jiya Alhamis ta kawo karshen sa toka sa katsi dake gudana a tsakaninsu tsawon lokaci.
A nasa bangaren, Gwamna Fubara ya bayyana zaman lafiya da aka samu a matsayin wata alfarma daga Allah, yana mai cewa hakan na nuni da sabon sahun ci gaba ga Jihar Rivers.
Duk da cewa rikicin ya samo asali ne tun bayan hawansa karagar mulki a watan Mayun 2023, inda ɓangarorin majalisar dokokin jihar mai biyayya ga Wike suka fara shirin tsige shi, lamarin da ya kai ga Shugaba Tinubu sanya dokar ta baci tare da dakatar da gwamnan jihar da rushe majalsar dokokin, da maye gurbuinta dana wucin gadi har na tsawon watanni shida, bisa zargin tabarbarewar tsaro da tsaikon gudanar da mulki.