Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna sun tabbatar cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata uwa da ƴaƴanta hudu

0 293

Rundunar ’Yan sanda a Jihar Kaduna sun tabbatar cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da wata uwa da ’ya’yanta hudu a Karamar Hukumar Chikun ta jihar.

Masu garkuwa da mutanen sun yi dirar mikiya a gidan matar suka tafi da ita da ’ya’yanta ne a unguwar Sabon Tasha kafin wayewar garin yau Asabar.

Kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed ya ce an yi garkuwa da su ne a daidai lokacin jami’an tsaro ke kokarin dakile wasu masu garkuwa a mutane a unguwar.

Ya ce Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta zage damtse domin kubutar da mutanen cikin aminci.

Ya ce da farko sun samu kiran neman agaji daga unguwar Sabo GRA a lokacin da masu garkuwar ke nema kutsawa gidan amma ’yan sanda suka fatattake su.

Abin takaici kuma ashe an kai hare-haren ne a lokaci guda, aka tafi da matar da ’ya’yanta. Ya ce tuni jamian yan sanda suka dukufa wajen bincike kan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: