Rundunar ƴansandan jihar Kano ta sanar da kama mutane 245 da ake zarginsu da aikata muggan laifuka

0 91

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da kama mutane 245 da ake zarginsu da aikata laifuka daban daban a fadin jihar, cikin kwanaki 40.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da rundunar ta gudanar a helikwatar hukumar.

Dikko ya ce a samamen da jami’an ‘yan sanda karkashin rundunar Puff-Adder, ke kai wa a kwaryar jihar domin kakkabe masu aikata laifi.

Wadanda aka kama ana zarginsu ne da aikata laifuuka da suka hada da Fashi da makami, satar mutane domin neman kudin fansa, da barayin shanu, da satar motoci, da ‘yan daba, da masu ta’ammali da muggan kwayoyi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: