Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta kama wani mutum bisa kisan wani hakimi

0 154

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani mutum mai suna Yusuf Abdallah bisa kisan hakimin Yantumaki da ke karamar hukumar Dan Musa a jihar.

A watan Yunin bara ne ‘yan bindiga suka kashe hakimin mai suna Alhaji Abubakar Atiku Maidabino.

Da yake gabatar da wasu da ake zargi da aikata laifuka a helkwatar rundunar a jiya da yamma, kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Gambo Isa, ya ce dan bindigar ya amsa laifinsa.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa, Yusuf Abdallah ya ce sun kashe hakimin ne saboda ya na katsalandan a cikin al’amuransu.

Da aka tambaye shi inda abokan aika-aikarsa suke, Yusuf Abdallah ya ce sun koma daji.

A wani cigaban kuma, rundunar ‘yan sandan a jiya ta ce ta samu nasarar fatattakar wasu gungun barayin mota da suka addabi jihohin Kano da Jigawa da Kaduna da Katsina, wadanda suke kai su Jamhuriyar Nijar domin sayarwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: