Rundunar ƴansandan Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar fasinjoji 12 tare da wani direba a karamar hukumar Ƴankwashi

0 173

Rundunar Yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar Fasinjoji 12 tare da wani Direban mota mai suna Ashiru Sani, biyo bayan hadarin mota da ya afku a jiya.

Kakakin rundunar yan sanda na Jihar nan ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Duste.

A cewarsa, yan sanda sun sami lamarin hadarin ne daga wata majiya mai karfi, kan cewa anyi hadarin mota a tsakanin garin Achilafiya zuwa Karkarna.

Haka kuma ya ce hadarin ya faru ne tsakanin Diraban wata mota kirar Golf mai suna Ashiru Sani mai shekaru 35 mazaunin kyauyen Fago na karamar hukumar Sandamu ta Jihar Katsina da kuma wani Direban wata mota Golf Wagon mai suna Bashir Ahmed mai shekara 25 mazaunin unguwar Tudu dake karamar hukumar Yan Kwashi ta nan Jihar Jigawa.

Kakakin yan sandan ya ce bayan hadarin da akayi a tsakanin Motocin biyu, Bashir Ahmed da fasinjojinsa sun kone kurmus, ta yadda baza’a iya gane su ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: