Rundunar ƴansandan jihar Kano ta kama wani matashin dan fashi da makami

0 163

Rundunar Yan sandan Jihar Kano ta kama wani Matashin dan fashi da makami mai suna Sabitu Ibrahim wanda aka fi sani da Aljan mazaunin Kaburma na karamar hukumar Dawakin Tofa ta Jihar.

Rundunar Opiration Puff-Adder ce karkashin jagorancin SP Buba Yusuf, sune suka yi nasarar kama Sabitu Ibrahim, kuma yana cikin sunayen mutanen da yan sanda suke nema ruwa a jallo, saboda aikata fashi da makami.

A binciken da rundunar ta gudanar, ta gano cewa Matashin ya amsa laifin cewa shine ya yi kokarin kashe wani Matashin mai babur din adaidaita sahu da Kebil, sai Matashin ya kubuta.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce rundunar ta kuma yi nasarar kama wasu matasa Abdullahi Suleiman dan shekara 28 mazaunin unguwar Gwale da kuma Abubakar Muhd dan shekara 21 mazaunin Hausawa.

Haka kuma ya ce yan sandan Jihar sunyi nasarar kwato babura 5 daga hannun wasu yan fashi da makami wanda aka kama a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: