Rundunar Sojin Kasa ta kori kimanin sojoji 3,000

0 102

Rundunar Sojin Kasa ta kori kimanin sojoji 3,040 sakamakon laifuka da dama, da suka hada da rashin ladabi, sayar da miyagun magani da fyade gami da kisa.

Wasu daga cikin sojojin, an sallame su ne, sakamakon kama su da laifin takardun bogi da rashin aiki tukuru, da fashin zuwa wajen aiki, gami da rashin gudanar da aikin Soji yadda ya kamata.

Haka Zalika, wasu Kuma an same su da Matsalar Shekaru, da sata, da Kuma yunkurin yin fyade gami da sakin masu laifi ba bisa ka’ida ba.

Kimanin Sojoji 1000 an sallame su ne sakamakon tafiya hutu ba tare da an basu ba, inda wasu soji 20 an kore su a dalilin, ‘ya’ya dake garesu a kasashen waje, da ciki ba tare da Aure ba,gami da yunkurin lalata da matan abokanan su, da boyewa makiya, zuwa zana’idar farar hula da cikin shigar soji, da batan Harsashi, bacci a wurin aiki da sauran su.

Sunayen wadanda Rundunar ta kora suna nan a cikin wani kundi mai shafi 90 da rundunar ta saki a Abuja.

Haka Zalika, Rundunar ta jaddada kudirin ta na magance matsalolin tsaro dake addabar wasu sassan kasar nan.

Jaridar Dimokuraɗiyya

Leave a Reply

%d bloggers like this: