Rundunar Sojin Najeriya ta kammala atisaye na musamman na horar da sojoji 604 karkashin shirin “Exercise Restore Hope” a Cibiyar Horar da Sojoji da ke Kachia a jihar Kaduna.
Horon na tsawon watanni shida ya kunshi dabarun yaki na zamani na bindiga, da kuma hanyoyin magance matsaloli ba tare da amfani da makami ba.
Babban Hafsan Soji, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ce sojojin sun nuna hazaka da biyayya tare da kwarewa a fannoni irin su kwarewar harbi da dabarun yaƙi. An zabi sojojin ne daga sassa daban-daban na rundunar, kuma za a tura su wuraren da ke fama da rikici domin ƙara ƙarfin rundunar a ayyukan da ke gudana a yanzu.