Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta gabatar da cakin kudi naira miliyan 18 da rabi ga iyalan jami’an ‘yansanda 25 da jami’an rundunar da suka mutu a bakin aiki.
Da yake gabatar da cakin kudin ga iyalan, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Oqua Etim, ya ce an bayar da kudaden ne a matsayin wani shiri na babban sufeton ‘yan sandan kasa Usman Baba Alkali domin yaye wahalhalun da suka shiga saboda rashin mazajensu.
A wani labarin kuma, a jiya ne zababben gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya tabbatar wa shugabannin addinin musuluncin jihar cewa zai kafa ma’aikatar kula da harkokin addini.
Nasir Idris ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da yake jawabi ga shuwagabannin musulmin da suka kai masa ziyarar hadin kai a gidan gwamnati dake Birnin Kebbi kan zaben sa a matsayin gwamna.
Ya ce idan aka kirkiri ma’aikatar za ta kawo hadin kan da ake bukata tsakanin malaman addini da al’ummar jihar.