Rundunar yan sanda Jihar Jigawa ta kama wani mai suna Yusuf Zubairu, wanda aka fi sani da Sallau dan shekara 26 a Duniya, kuma mazaunin kyauyen Baldi ta Karamar hukumar Sule Tankarkar bisa zarginsa da kashe matarsa mai suna Fatima Hardo bayan sun samu rashin fahimtar juna.

Kakakin rundunar yan sanda Jihar Jigawa ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema Labarai a Dutse.

A cewarsa, ofishin rundunar yan sanda sun sami rahoto daga wani mai suna Bulama Muntari Ubale, inda ya bayyana musu cewa wani mai suna Yusuf Zubairu, ya kashe matarsa mai suna Fatima Hardo Dare yar shekara 23, bayan sun samu sabani.

An rawaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da suka sami sabani, inda mutumin ya yi amfani da Sanda da wajen dukan ta a kanta.

Haka kuma, an bayyana cewa a lokacin da Sallau suke rigima da marigayiyar, sai wata mai suna Rabi Lawan, ta shigo domin raba rigimar inda itama ya doke ta da sanda tare da raunata ta.

ASP Lawan Shiisu Adam, ya ce bayan samun labarin faruwar lamarin ne suka dauki matar zuwa babban Asibitin Kwantarwa na Gumel, inda babban Likita ya tabbatar musu da mutuwarta, inda ya kara da cewa wacce aka jiwa ciwon tana cigaba da samun kulawar likitoci.

Kazalika, ya ce an kama Mijin marigayiyar, inda ake cigaba da zurfafa bincike domin gano gaskiya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: