Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta ce maharan sun harbe jami’anta biyu tare da kona gawarwakinsu

0 64

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta ce maharan sun harbe jami’anta biyu tare da kona gawarwakinsu.

A cewar ‘yan sandan, har yanzu ba a ga wani jami’i guda daya ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce jami’an da aka kashe na tafiya ne a cikin mota tare da wasu jami’ai biyar da kuma wasu direbobin fararen hula uku a yayin da wasu ‘yan bindiga suka yi musu kwanton bauna a ranar Alhamis a wasu kayuka a jihar Anambra.

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafar sadarwa ta WhatsApp ya nuna yadda ‘yan bindigar ke zagaye gawarwakin jami’an biyu a tsakiyar hanya, kuma kusa da gawarwakin akwai wasu tayoyin mota da aka jefar.

Tochukwu ya ce sauran Jami’an ‘yan sandan sun tsira daga kwanton baunar sun kuma samu nasarar kubutar da biyu daga cikin direbobi fararen hula uku.

Ya ce ‘yan bindigar sun kai hari kan tawagar masu aikin ceto, inda suka yi ta jefa bama-bamai a kan motocin ‘yan sanda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: