Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta musanta rahotannin kashe wasu ‘yan kasar Amurka a jihar.
Kakakin rundunar, Tochukwu Ikenga, a wata sanarwa da ya fitar jiya a Onitsha, ya ce babu wani dan Amurka a cikin ayarin motocin da ‘yan bindiga suka kai wa hari a jiya.
‘Yan bindigar sun bude wuta kan ayarin motocin ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka da ke karamar hukumar Ogbaru a jihar.
Tochukwu Ikenga ya ce an kashe ‘yan sandan tafi da gidanka biyu da ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka biyu da ke cikin ayarin motocin tare da kona gawarwakinsu da motocinsu.
A cewarsa, rundunar hadin guiwa ta jami’an tsaro ta fara aikin ceto da bincike don gano inda ‘yan bindigar suke domin ta kama su. Ya kuma ba da tabbacin cewa za a ci gaba da yaki da masu tada kayar baya a jihar har sai an samu kwanciyar hankali.