- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi a jiya ta yi gargadi kan gudanar da jerin gwano a jihar da ke fakewa da ganin watan Ramadan.
Gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Mohammed Wakil, inda ya bukaci al’ummar jihar su ci gaba da baiwa ‘yan sanda goyon baya wajen yaki da miyagun laifuka.
A cewar sa, rundunar ta ja hankali ne kan wani shiri da wasu bata-gari suka yi suna na farin cikin ganin jinjirin watan Ramadan domin kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.
Ya kuma kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Umar Mamman Sanda, don haka ya gargadi masu kitsa wannan shiri da su kau da kai daga wajen ‘yan sanda za su fuskanci turjiya.