Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta gargadi masu ababen hawa kan yadda suke mummunan lodi da kuma matsalar tukin yara

0 73

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta gargadi masu ababen hawa kan yadda suke lodi fiye da kima da kuma matsalar tukin yara.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun kakakin rundunar, ASP Lawan Shiisu Adam.

Ya ce an yi gargadin ne domin rage yawan hadurran da ke faruwa a fadin jiharnan.

Shiisu Adam ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Sale Tafida, ya umurci dukkan jami’an ‘yan sanda na shiyyar da su fara sintiri sosai.

Sai dai ya umarce su da su kamo tare da gurfanar da direbobi masu lodin da ya wuce kima da masu karancin shekaru a fadin kananan hukumomi 27 na jiharnan, ba tare da bata lokaci ba.

Aliyu Tafida ya kuma jaddada kudirin ‘yan sanda na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: