Labarai

Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu yan bindiga 5 wanda suke addabar jihohin Jigawa da Kano ta fuskar yin garkuwa da mutane

Rundunar yan sandan Jihar Jigawa ta kama wasu yan Bindiga 5 wanda suke addabar Jihohin Jigawa da Kano ta fuskar yin garkuwa da mutane a yankunan.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar Jigawa ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse.

A cewarsa, yan sanda sun samu bayanan sirri kan wani Kasurgumin mai garkuwa da mutane mai suna Yusuf Wakili wanda akafi sani da Rago inda suka samu nasarar kamashi a karamar hukumar Ajingi ta Jihar Kano.

Haka kuma ya ce sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutanen ne tare da Inusa Jibrin, Alh Tahir Zango, Sabo Abdullahi Alias Sabo Gara da Suleman Garba wand aka fi sani da Manu Dogo.

ASP Lawan Shiisu Adam, ya ce Mutanen sun amince da aikata laifukan sace-sacen mutane a Jihohin Kano da Jigawa.

Yan sanda sun kwato bindiga 1 tare da wasu harsashe daga hannun yan bindigar.

Kakakin rundunar yan sandan ya ce an tura mutane zuwa sashen bincikar manyan laifuka.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: