Labarai

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce wasu mutane da aka gani ana dorasu cikin motocin sojoji guda biyu a wani faifan bidiyo ba ’yan fashin daji bane

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna a jiya ta ce wasu mutane da aka gani ana dorasu cikin motocin sojoji guda biyu a wani faifan bidiyon da ya yadu a shafukan sada zumunta a karshen mako ba ’yan fashin daji bane.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Yekini Ayoku, ne ya bayyana hakan a jiya a yayin wani taron zaman lafiya da ya samu halartar kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan da shugaban karamar hukumar Chikun da sojojin runduna ta 312.

Ya ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wani matsugunin Fulani a Kakura dake gundumar Kujama a karamar hukumar Chikun ta jihar, inda suka kashe dan uwan ​​mai garin. Daga nan ne ‘yan bindigar suka je wani kauye suka yi awon gaba da shanu.

Wasu ’yan banga daga garin da aka kashe dan uwan ​​mai garin sun bi sahun ‘yan bindigar. Kazalika Fulani makiyayan sun je neman shanunsu da aka sace.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: