Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi da dakon man fetur ga ‘yan bindiga a jihar Katsina

0 41

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da dakon man fetur ga ‘yan bindiga a jihar Katsina, daga Kano.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa jiya a Kano.

Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Musbahu Rabi’u mai shekaru 31 da Jamilu Abdullahi mai shekaru 37 dukkansu mazauna karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Haruna-Kiyawa ya ce an kama wadanda ake zargi da motoci biyu dauke da man fetur a cikin jarkoki masu cin lita 25 da aka boye cikin buhuhunan sukari.

Haruna-Kiyawa ya yi bayanin cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Samaila Shu’aibu-Dikko, a halin yanzu, ya ba da umarnin yin bincike kan lamarin, bayan haka za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga masu aiki a gidajen mai a jihar da su guji sayar da mai da yawa cikin jarkoki ga wadanda ba a san su ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: