Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta dakile wani yunkurin yin garkuwa da dagaci

0 104

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta ce ta dakile wani yunkurin yin garkuwa da dagacin Garun-Babba, Alhaji Abdulmuminu Mudi da ke karamar hukumar Garun-Mallam a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abdullahi Haruna-Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya a Kano.

A cewar kakakin, an samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga a kan babura, sun sace dagacin kauyen.

Ya kara da cewa da samun rahoton, mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda na rundunar, Abubakar Zubairu, ya aika da tawagar ‘yan sanda.

Haruna-Kiyawa ya bayyana cewa, nan take tawagar ta bi sahun wadanda suka aikata laifin wanda hakan ya sa suka ajiye hakimin kauyen tare da barin babura uku kuma suka tsare.

A cewar sanarwar, mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan ya yabawa jami’an ‘yan sandan bisa kwazon da suka nuna cikin gaggawa, sannan ya umarce su da su kara kaimi wajen kamo wadanda ake zargin da suka tsere.

Leave a Reply

%d bloggers like this: