Rundunar yan sandan jihar Katsina sun kashe wani babban dan bindiga tare da kwato shanu 50 wanda ya kwace

0 25

Rundunar Yan sandan Jihar Katsina sun kashe wani dan bindiga tare da kwato shanu 50 mallakin Alhaji Ibrahim Maikudi, na kyauyen Gago, a karamar hukumar Dutsinma, wanda yan bindigar suka sace.

Da yake jawabi ga manema labarai a Ofishin yan sanda da ke Katsina, Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Gambo Isah, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1 na Dare, lokacin da yan bindigar su kimanin 40 suka kaiwa garin hari tare da sace shanun.

Mutanen garin sun kira Kwamandan Rundunar Yan Sandan Shiyar Dutsinma, domin kawo musu dauki, inda kuma yan sandan suka yi nasarar zuwa garin akan lokaci tare da kashe dan bindiga 1 da kuma kwato shanu 50 a lokacin artabun.

Haka kuma ya ce yan bindigar sun bar bindiga kirar AK-47 guda 1 sakamakon tserewar da suka yi.

Kazalika, ya ce wasu yan bindigar da dama sun tsere da raunikan harbi a jikin su, inda ya kara da cewa Jami’an yan sandan suna cigaba da bibiyar wanda suka tsere domin kamo su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: