Rundunar yan sandan jihar Neja sun kubutar da wani shugaban wata shiyya na jam’iyyar APC

0 90

Rundunar Yan Sandan Jihar Neja sun kubutar da shugaban jam’iyyar APC na shiyyar C, Alhaji Aminu Musa Bobi, daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

A ranar 7 ga watan Agusta da misalin karfe 2:00 na dare, wasu mutane dauke da makamai suka kai hari kan wanda aka kubutar da din tare da direbansa, Malam Nasiru Bobi, a hanyarsu ta zuwa gona a kan hanyar Ukuru a cikin yankin Bobi na Karamar Hukumar Mariga.

Kakakin ’yan sanda na jihar, DSP Wasiu Abiodun ne, ya sanar a da hakan a ranar Asabar inda ya ce an kubutar da dan siyasan ne a jiya Juma’a.

DSP Abiodun ya ce, an kubutar da wanda aka sace din daga dajin, sannan aka kai shi Babban Asibitin Kontagora domin duba lafiyarsa, ana kuma ci gaba da kokarin gano masu laifin.

Haka kuma ya ce an harbi direban a kafa kuma maharan sun kyale shi, amma suka yi awon gaba da shugaban.

A cewarsa, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja ta tara jami’anta da sojoji da ’yan banga zuwa yankin domin farautar ’yan bindigar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: