Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta samu nasarar daƙile wasu hare-haren yan bindiga

0 79

Rundunar yan sandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar nan, ta ce ta samu nasarar daƙile hare-haren Yan bindiga a faɗin ƙananan hukumomin jihar guda hudu, tare da kuɓutar da wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Yan sandan jihar SP Mohammed Shehu, ya fitar ya ce Yan bindigar sun yi ƙoƙarin kai hare-hare a wasu ƙauyuka da ke ƙananan hukumomin Maru, da Bungudu, da Tsafe da kuma ƙaramar hukumar Bukkuyum.

Ya ce jami’ansu sun samu nasarar daƙile hare-haren ta hanyar bayanan sirri da suka samu.

SP Mohammed Shehu, ya ƙara da cewa daga ranar Juma’a zuwa Lahadi sun samu bayanan sirri da ke nuna cewa Yan bindigar na shirin ƙaddamar da hare-hare a ƙauyukan da ke wanɗannan ƙananan hukumomi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: