Rundunar ’yan sandan Kano ta haramta wa ’yan banga da mafarauta gudanar da ayyukan samar da tsaro

0 157

Rundunar ’yan sandan Kano ta haramta wa ’yan banga da mafarauta gudanar da ayyukan samar da tsaro a jihar.

Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar a ranar Alhamis cewa ba a yarda ’yan banga ko mafarauta su yi aikin samar da tsaro a ko’ina a jihar ba.

Rundunar tace an dauki matakin ne domin kawar da shakku tare da dakatar da ’yan banga da mafarauta da dangoginsu daga shiga cikin aikin samar da tsaro.

Sanarwar ta fito ne a yayin  da Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano take shirin yanke hukunci kan shari’ar dambarwar masarautun jihar.

Rundunar ta ce ya zama wajibi ta ba wa jama’ar jihar cikakken tsaro daga masu neman tayar da fitina, lura da yadda shari’ar ke sa mutane zullumi.

Kiyawa ya kara da kira ga jama’a da su ba da hadin kai ga jami’an tsaro da ke aikin tabbatar da doka da oda a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: