Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce jami’anta sun kashe wasu ‘yan bindiga shida a hare-haren da suka kai a Abuja da Jigawa, inda suka kuma ceto wata mata mai shekaru 80 da aka yi garkuwa da ita.
A Jigawa, an kashe ‘yan bindiga biyar bayan da suka sace matar daga Kano tare da kokarin ketarawa da ita zuwa dajin Jigawa, amma jami’an ‘yan sanda sun dakile harin tare da kama wasu biyar ciki har da shugaban gungun.
A Abuja kuwa, an dakile wani harin fashi da makami a Maitama inda aka kashe fitaccen ɗan fashi, Abdulmininu Bello (wanda ake kira Babanle), sannan aka kama wasu bakwai.
Kayan da aka gano sun hada da bindigogi, da motoci, da alburusai, yayin da Sufetan ‘Yansanda, Egbetokun, ya yaba da kokarin jami’an tare da kiran jama’a su ci gaba da bayar da hadin kai wajen tabbatar da tsaro.