Rundunar ‘yan sandan ta kasa ta ce ba za ta tsoma baki a cikin binciken da akeyiwa Abba Kyari ba

0 74

Rundunar ‘yan sandan ta kasa ta ce ba za ta tsoma baki a cikin binciken da akeyiwa dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sandan na kasa Abba Kyari ba, biyo bayan kama shi, bisa zargin sa da hannu a hada-hadar miyagun kwayoyi.

Mukaddashin kakakin rundunar yansanda ta kasa CSP Muyiwa Adejobi, ne ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, hakan a jiya Talata a babban birnin tarayya Abuja.

Inda ya ce rundunar ‘yan sanda ba za ta iya yin la’akari da duk wata haramtacciyar yarjejeniya da wani jami’in rundunar da aka dakatar ya yi ba.

Amma jami’an yanasanda suna iya bakin kokarinsu domin jin karin bayani daga bakin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.

Kafin hakan dai Rundunar ‘yan sandan ta mika DCP Abba Kyari da aka dakatar da wasu jami’a hudu ga hukumar ta NDLEA a ranar Litinin, sa’o’i kadan bayan hukumar ta bayyana cewa tana neman sa ruwa a jallo.

An kuma zarge su ne da laifin cin hanci da rashawa da kuma yin katsalandan kan abubuwan da suka shafi muggan kwayoyi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: