Rundunar ‘yansanda ta kasa ta kori jami’an ‘yansanda 9 daga aiki bisa zargin kitsa yajin aikin ‘yansanda.

Sufeto Janar na ‘yansanda, Usman Alkali Baba, ya amince da korar da aka yiwa ‘yansanda cikin wata sanarwa da kwamishinan harkokin ‘yansanda a helkwatar ‘yansanda dake Abuja, biyo bayan shari’ar da aka yi musu.

An aika da sanarwar zuwa wasu ofisoshin ‘yansanda dake sassan kasarnan.

‘Yansanda sun yi barazanar tafiya yajin aiki bisa kin fara aiwatar da karin albashi na kashi 20 cikin 100 wanda majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da shi a watan Disambar bara. An tsara fara biyan karin albashin a watan Janairun bana.

Bayan yaduwar labarin shirin tafiya yajin aikin, sufeto janar na ‘yansanda ya gargadi jami’an ‘yansanda da suyi watsi da yajin aikin ko kuma su shirya fuskantar hukunci.

Usman Baba ya kuma aika da mambobin tawagar gudanarwa zuwa ofisoshin ‘yansanda daban-daban domin kwantar da hankalin ‘yansanda tare da alkawarin gaggauta biyan karin albashin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: