Ruwan sama da kankara sun lalata gonakai da gidaje a mazabun Dutsen-Kura da Kanya da kuma Gozaki da ke karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina

0 94

Ruwan Sama da Kankara sun Lalata Gonakai da Gidaje a Mazabun Dutsen-Kura da Kanya da kuma Gozaki da ke Karamar Hukumar Kafur ta Jihar Katsina.

Wani Mazaunin garin Gozaki mai suna Mallam Abdullahi Gozaki, shine ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce babu wani mutum da ya taba ganin irin wannan Iftila’i a rayuwar sa a wannan yankin.

A cewarsa, Gonakai da rufin Gidaje da kuma Gilasan Motoci sun lalace, sakamakon kankarar mai karfin gaske da aka samu wanda ta shafe tsawon Mintuna ana yi.

Haka kuma ya bayyana sunayen gururuwan da aka samu irin wannan iftila’I wanda suka hada da Gidan Danwada, Gidan Sabo, Kabalawa, Unguwar Tsamiya, Dandabo, Unguwar Maigarma, Unguwar Wanzamai and Unguwar Fulani.

Da ya ke Jawabi kan faruwar Lamarin, Shugaban Karamar Hukumar Kafur Alhaji Garba Kanya, ya ce kankarar ta Lalata fiye da Gonakai 300 a wasu garuruwa da abin ya shafa.

Haka kuma ya ce amfanin Gonaki na Miliyoyin Kudade ne suka lalace ciki harda Masara da Gero da Shinkafa da Waken Suya da Albasa da Tattasai a lokacin da ake kokarin Girbar su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: