Ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 110 tare da jikkata wasu da dama a kauyen Kasaza da ke cikin yankin Fizi na gabashin lardin Sud Kivu a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, kamar yadda gidan rediyon Okapi da ke ƙarƙashin goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ya ruwaito.
Aƙalla gidaje 150 ne ruwa ya shafe a sakamakon ruwan sama da aka samu tsakanin ranakun 8 zuwa 9 ga Mayu, lamarin da ya bar fiye da mutum 850 ba tare da matsuguni ba.
Mai kula da yankin Fizi, Samy Kalonji, ya nemi agaji domin binne mamatan da kuma taimakawa iyalan da suka rasa matsugunansu.
“Jikunan mutane da dama har yanzu na kwance a ƙasa. Muna buƙatar akwatin gawa da taimako domin a samu a binne su cikin mutunci,” in ji Kalonji.
A wani labari makamancin haka, mutane 62 sun mutu a daren 8 zuwa 9 ga Mayu bayan ambaliya daga rafin Kasaba ta mamaye wani ƙauye daban da ke cikin yankin Fizi, kamar yadda shafin Media Congo mai zaman kansa ya bayyana.
Jami’an yankin sun ce aikin ceto yana fuskantar cikas sakamakon lalacewar hanyoyi da kuma nisan wurin da abin ya faru.
Wannan na zuwa ne ƙasa da wata guda bayan da aƙalla mutum 30 suka mutu sakamakon ruwan sama da ambaliya a babban birnin ƙasar, Kinshasa.