Ruwan sama ya rushe tare da lalata gidaje 760 a karamar hukumar Gumel

0 216

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya rushe tare da lalata gidaje 760 a karamar Hukumar Gumel.

Shugaban karamar Hukumar Ahmed Rufai Sanusi ya bayyana hakan a lokacin rangadin duba wuraren da ruwan ya yi ta’adi.

Yace barnar ruwan ta shafi mazabun yankin 11, inda yayi alkawarin gabatar da rahotan ambaliyar ruwan ga hukumomin da abin ya shafa domin daukar matakin tallafawa.

A wani labarin kuma, za a kaddamar da tallafin gwamnatin tarayya na naira dubu biyar biyar ga masu karamin karfi a karamar hukumar Gumel.

Jagorar shirin a karamar hukumar, Hajia Aisha Yau Gumel ta bayyana hakan a lokacin taron jamian kula da shirin na karamar hukumar.

Ta ce shirin zai fara a ranar 23 ga wannan watan, idan za a biya duk wanda yake cikin shirin, naira dubu biyar-biyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: