Sabon Gwamnan Jihar Zamfara Ya Zargi Bello Matawalle Da Barin Baitul-malin Jihar Da Basussuka Masu Dimbin Yawa

0 83

Sabon gwamnan jihar Zamfara da aka rantsar, Dauda Lawal Dare, ya zargi magabacinsa Bello Matawalle da barin baitul-malin jihar da basussuka masu dimbin yawa.
Dauda Lawal ya bayyana hakan ne jim kadan bayan an rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar a jiya.
Gwamnan, ya yi alkawarin kawo ci gaba cikin sauri tare da magance dimbin kalubalen da jihar ke fuskanta.
Dauda Lawal, wanda ya ce ya zo ne domin ceto jihar Zamfara, ya kuma yi kira ga matasa da su guji duk wani nau’in miyagun ayyuka.
Bello Matawalle da mataimakinsa Hassan Nasiha ba su halarci bikin rantsarwar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: